31 Maris 2020 - 16:05
Ma'aikatar Tsaron Iran Ta Kaddamar Da Sabuwar Na'aurar Gano Cutar Coronavirus

A kokarin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi na dakile yaduwar cutar nan ta Coronavirus a kasar, Ma'aikatar tsaron kasar ta kaddamar da wata na'urar gano cutar cikin kankanin lokaci.

(ABNA24.com) Yayin da yake sanar da hakan, kwamandan da ke kula da fada da cutar coronan a Ma'aikatar tsaron kasar ta Iran Birgediya Janar Azizi Delshad ya bayyana cewar na'urar wacce kwararrun kasar ta Iran suka samar tana da karfin gano cutar coronavirus din cikin sa'oi uku kacal.

Janar Delshad ya kara da cewa tun a farko-farkon watan Maris din nan ne aka samar da na'urar to amma a halin yanzu bayan gwajin da aka gudanar kanta an tabbatar da yanayin aikinta kuma tuni ma'aikatar kiwon lafiya ta Iran din ta amince da a ci gaba da samar da ita don rabawa bangarori daban-daban a kokarin da ake yi na dakile cutar ta Covid-19.

Kwamandan sojin ya ce a halin yanzu dai wannan na'urar za ta iya gasa da sauran makamantan ta da ake da su a duniya, yana mai cewa Ma'aikatar tsaron tana da karfin samar da adadin da ake bukata a ciki da wajen kasar ta Iran don yakar wannan annobar.

342